Shugaban sabuwar hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, NMDPRA, Farouk Ahmed, ya alakanta hauhawar farashin iskar gas da rashin sanya hannun jari a fannin tsawon shekaru.
Faruk Ahmed, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin kaddamar da shi a matsayin shugaban NMDPRA yayin da Gbenga Komolafe ya zama shugaban Nigeria Upstream Regulatory Commission, NURC.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kaddamar da shi, Gbenga Komolafe, ya ce hukumarsa ba ma iya harkokin hakar mai a kan tudu kadai ba, har ma da harkokin kasuwancinsa.
Ya ce hukumar za tai aiki domin tabbatar da cewa Nigeria ta cika bukatar kungiyar OPEC na fitar da mai da kuma habbaka samu a bangaren musamman daga tashin farashin man da ake samu.
A bangarensa, Faruk Ahmed ya bayyana cewa NMDPRA za tai gaggawa wajen aiki da masu ruwa da tsaki domin saurin magance matsalar tsadar iskar gas.