Shugaban masu rinjaye a Majalissar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC a babban zaben shekarar 2023.
Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Doguwa/Tudun Wada a jihar Kano, ya samu tikitin takarar ne bayan lashe zaben fidda gwani domin wakiltar mazabar ta sa a karo na 7.
Dan Majalissar ya fara kasancewa Dan Majalissa ne a tsohuwar jamhoriya ta uku.
Ya samu nasarar dawowa a majalissar ne a jamhoriya ta 4, kuma tun shekarar 2003 yana majalissar har kawo yanzu.
Shugaban masu rinjayen a Majalissar Wakilan, an zabe shi a matsayin dan Majalissar Wakilai ne tun a shekarar 1992, jim kadan bayan kamala aikin bautar kasa NYSC da yai.
Da yake magana da manema labarai bayan samun nasarar zaben fidda gwanin da yai, Doguwa ya ce, “wannan ne dama ta 7 da na samu ta tsayawa takarar Majalissar Wakilai ba tare da hamayya ba.”
Dan Majalissar ya nuna farincikinsa ga shugabanni da mambobin jam’iyyar APC na mazabarsa da ma Jihar Kano gaba daya saboda goyon bayan da suke ba shi da kuma amincewa da kwarewarsa da sukai wajen wakiltar mutanensa.