Sanannen dan wasan Hausa (Kannywood), Sani Garba SK ya rasu yau a garinsu na Kano.
A ‘yan kwanakin nan dai an ta yada labarin mutuwar jarumin a tsakanin masu kallon fina-finan Hausa.
Hakan ya biyo bayan jinyar da yake fama da ita wadda aka ce ta samo asali daga matsalar ciwon suga da kuma koda.
Wani jarumi a masana’antar Kannywood, Abdul Smart ya bayyanawa BBC Hausa cewa, Sani SK ya rasu a yayin da ake kokarin yi masa wankin koda a asibitin Kwararru na Nassarawa da ke Kano.
Marigayi Sani Garba SK dan asalin unguwar Zage ne da ke tsakiyar birnin Kano, kuma ya dade yana fitowa a finafinan Kannywood kuma ya yi suna.