Daga: Ahmed Ilallah
Bana a tarihin siyasar Jihar Jigawa babbar jama’iyya mai mulki ta bawa Jigawa yankin Arewa maso Gabas, wato yankin Hadejiawa takarar gwamna, wanda a bisa tarihi babu wata jama’iyya wadda tayi hakan a baya.
Kamar yadda na fada a baya, a cikin rubutu na MENENE ZUNUBIN BAHADEJE? A shekarun Jigawa babu wani daga yankin Hadejia da yayi gwamna a Jigawa, a misali Alhaji Sule Lamido a PDP ya yi takarar gwamna har sau biyu, ya yi nasara, bayan ya sauka ya tsayar da Malam Aminu Ringim daga Arewacin Jigawa har sau biyu, amma a yau jama’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru ta bawa yankin Hadejia damar yin takarar gwamna a zabe mai zuwa – Malam Umar Namadi ya yi nasarar cin zaben fidda gwani da gagarumar nasara, wanda daga dukkan alamu an zo lokacin da wannan yanki zai yi gwamna a Jigawa.
Amma babbar jama’iyya mai adawa ta PDP a Jigawa a wannan karon ma ta mai da takarar gwamna zuwa Jigawa ta tsakiya, wanda a sabon salo a wannan karon ma dan babban jagora ne Mustapha Sule Lamido zai gaje shi, duk da cewa dakarun sa na siyasa suna wannan yankin.
Duk da cewa ba da takara ko yin takara ba shine yin gwamna ba, amma tabbas alama ce da kuma tirba ta zama gwamna.
Adalci ne da kuma karfafa hadin kan mutanen Jigawa wajen sanyawa da bawa kowane mutum da kowane yanki damar ba su tasu gudunmawar wajen gina tasu jihar.
Tarihin Jihar Jigawa ya nuna irin gudunmawar da wannan yanki na Jigawa ta Gabas
ya bada wajen ginawa da ci gaban Jigawa, kama ta samar da kwararru a kowane fanni, gina tattalin arziki, noma da samar da masana’antu.
To amma tambayar anan ita ce, shin za a iya cewa a wannan karon za a iya cewa Badaru ya shafewa Hadejiawa hawayen su kuwa?
Ahmed Ilallah ya rubuto ne daga Hadejia, Jihar Jigawa