For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dansanda Ya Bindige ‘Yansanda 6 Har Lahira Bayan Samun Sabani Da Matarsa A Maiduguri

Wani jami’in dansanda mai suna Saja Bello ya bindige tare da kashe a kalla yan sandan sintiri na mobile guda shida a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a rukunin gidaje da ke kwalejin ‘yansanda ta Hedkwatar ‘Yansanda a Maiduguri a cewar majiyoyi.

Wani babban jami’i ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa a halin yanzu ana can an tsare jami’in a sashin binciken manyan laifuka, SCID.

An gano cewa dansandan ya samu rashin jituwa da matarsa a gida kafin faruwar lamarin.

Wata majiya daga iyalansa ta ce Saja ya samu rashin jituwa da matarsa kuma makwabta sun yi kokarin sulhunta su amma bai saurare su ba.

“Sun dade suna samun rashin jituwa da matarsa; mun yi kokarin sulhunta su amma bai yarda ba.

“Matar ta fada wa iyayenta cewa Saja ya doke ta; ta bar masa gidansa. Matar ta bar gidan saboda rashin kyautatawa daga mijinta.

“Ya fara harbe-harbe yana barazanar zai kashe kowa. Ya bindige mutune, yansanda shida sun mutu wasu biyu suna asibiti ana musu magani.

“Ya kona gidaje biyu da dakuna takwas kuma ya harbi surukinsa,” in ji majiyar.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yansandan jihar Borno amma hakan bai yiwu ba domin wayarsa na kashe a lokacin hada wannan rahoton.

(LEGIT HAUSA)

Comments
Loading...