Aminu Dantata da Aliko Dangote sun bayar da tallafin naira biliyan 2.5 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Alhaji Aminu Dantata ya ba da gudunmuwar naira biliyan 1.5 ne lokacin da ya jagoranci tawagar daga Kano zuwa gidan gwamnati a Maiduguri ranar Talata don jajantawa mutanen da abin ya shafa.
Ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum, gwamnatin jihar, da al’ummar Borno, musamman dangin da suka rasa ƴan’uwansu a ambaliyar.
Dantata ya bayyana damuwarsa game da matsalar tattalin arziƙin Najeriya, yana mai kira ga shugabanni su tuba su ji tsoron Allah.
Ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Borno da Najeriya baki daya.
A jawabinsa, Gwamna Zulum ya nuna godiyarsa ga Dantata, yana mai cewa ziyarar ta zama wata salama da samun goyon baya a lokacin jarrabawa.
Haka kuma, Dantata ya bi sahun ɗansa, Alhaji Aliko Dangote, wanda shima ya bayar da gudunmuwar naira biliyan 1 don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.