For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Darajar Jimilar Cinikayyar Duniya Ta Kai Dala Tiriliyan 7.7 A Watanni Ukun Farkon 2022

A ranar Alhamis da ta gabata ne, taron karawa juna sani na cinikayya da samar da ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da rahoton dake cewa, darajar jimillar cinikayyar duniya ta kai dalar Amurka tiriliyan 7.7 a watanni ukun farkon shekarar 2022, adadin da ya karu da dala tiriliyan 1, la’akari da abun da ya faru watanni ukun farkon shekarar 2021, kuma karuwar cinikayyar yankuna daban daban tana cikin matsayi mai karfi.

Taron ya kuma yi hasashen cewa, ko da yake cinikayyar duniya zata ci gaba da karuwa, amma saurin karuwar cinikayyar zai ci gaba da raguwa a watannin gaba da wadancan, kuma hauhawar farashin kayayyaki da rikicin Rasha da Ukraine ya haddasa, zai yi tasiri ga cinikayyar duniya, da habakar kudin ruwa na bankuna, yayin da dabarun karfafa tattalin arziki a hankali, na iya yin mummunan tasiri ga kasuwancin duniya.

(CRI HAUSA)

Comments
Loading...