Daraktan Janar na Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Salihu Mohammed Lukman, ya ajjiye aiki saboda rikice-rikicen da suka dabaibaiye jam’iyyar game da Babban Taronta na kasa.
Lukman ya ajjiye aikin ne a yau Litinin saboda rabuwar da aka samu a tsakanin gwamnonin jam’iyyar lokacin zaman da sukai a daren jiya Lahadi a Abuja.
Wasu majiyoyi da suka bukaci a boye sunayensu, sun bayyana cewa, tuni Lukman ya mika takardar ajjiye aikin nasa ga Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
KU KARANTA: APC Ta Sa Ranar 25 Ga Fabarairu Domin Zaben Shugabaninta Na Kasa
Majiyar ta sanar da cewa, wasu daga cikin gwamnonin suna bukatar ajjiye aikin Lukman ko kuma ma a kore shi, abin da ya jawo ajjiye aikin nasa.
An gano cewa, duk da mafi yawa daga cikin gwamnonin suna son Lukman ya cigaba da kasancewa a kujerar, kadan daga cikinsu sun takura sai ya tafi.