An gurfanar da mutane 4 a gaban Kotun Majistare da ke Yola saboda kisan Adamu Ahmadu dan shekara 28 wanda sukai kuskuren zarga da satar wayar salula.
Marigayi Adamu, wanda dan gidan wani mai gadin Ma’aikatar Yada Labarai ne ta Adamawa, ya fuskanci zargin satar wayar ne daga Hamidu Umar dan gidan saukakken digacin Damare da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
Hamidu ya yi zargin Adamu ya sace masa wayar ne a ranar 22 ga watan Janairun da ya gabata.
Duk da a lokacin, marigayin ya musanta zargin, amma Hamidu ya matsa masa cewa sai ya fito da wayar.
An gano cewa, Hamidu mai shekaru 55 tare da wadansu abokansa guda 3 sun yanke shawarar wahalar da Adamu har sai ya amsa laifin.
Sauran mutane ukun sune: Sholle Manas, Faisal da kuma Nahau.
Hamidu, da taimakon Faisal da Nahau, sun dauki Adamu zuwa wani kango da misalin karfe 5:30 na yamma inda suka gana masa azaba da katakaye da kuma fasassun bulo.
An gano cewa, a dalilin wannan azabtarwa, Adamu ya samu karaya a hannayensa da sauran ciwuka wadanda suka yi sanadiyyar mutuwarsa.
Lokacin da aka kama wadanda ake zargin a ranar 15 ga Fabarairun nan, Hamidu ya musanta zargin, yayin da
Sholle wanda da farko ya musanta, ya dawo ya karbi laifin.
Da yake tabbatar wa da kotu laifinsa, Sholle ya ce, ya hadu da Hamidu ne da sauran biyun suna dukan marigayin, inda ya kara da cewa, sai Hamidu ya gaiyace shi domin ya shiga shima a yi da shi.
Mutum biyu cikin hudun da ake zargi wato Nahau da Faisal sun tsere ba tare da an gurfanar da su a gaban kotunba.
Rahotannin farko sun nuna cewa, sabon digacin Damare, Sahabo Umar ne ya ceci Adamu, wanda kuma ya mika maganar ga ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda na Wuro.
Rahoton ya nuna cewa, bayan aikata waccan aika-aikar ne Hamidu ya koma gidansa, inda ya sami wayarsa a kan doguwar kujera a falonsa.
Rahoton ya cigaba da cewa, an garzaya da marigayin zuwa asibitin Federal Medical Center, Yola domin ba shi kulawa, amma daga bisani ya rasu a ranar Lahadi 13 ga watan Fabarairun da muke ciki, kuma an binneshi kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.
Alkalin Kotun Majistaren, Dimas Gwamu, ya dage sauraron karar zuwa rana ta gaba, domin yanke hukunci ga wanda ya amsa laifinsa da kuma cigaba da tuhumar sauran.
(PUNCH)