For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dattawan Arewa Sun Yi Kira Da A Rushe Hukumomin Zabe Na Jihohi

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi kira ga Majalissun Tarayyar Nigeria da su saka batun rushe hukumomin zabe na jihohi tare da dorawa Hukumar Zabe ta Kasa mai Zaman Kanta alhakin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihohi.

Kakakin Kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya gabatar ranar Laraba, bayan kammala zaman tattaunawar kungiyar wanda Shugaban Kungiyar, Prof. Ango Abdullahi ya jagoranta.

Dr. Hakeem ya kuma bayyana cewa, “Kungiyar ta jinjinawa duk ‘yan Nigeria wadanda ke kokarin dawo da martabar Demokaradiyarmu. Yanzu ya ragewa ‘yan siyasa da sauran shugabanni da su gudanar da siyasar da ke samar da daidaito, gaskiya, cancanta da kuma adalci, ta hanyar gudanar da yakin neman zabe na nuna hadin kai da kuma nuna kishi a shiryeshiryen zaben shekarar 2023. Mutanen Arewa na son yin aiki da sauran ‘yan Nigeria domin fito da tsarin jagoranci bisa cancanta da kishin kasa wanda zai dawo da karfin guiwar kasarmu na rayuwa da samun cigaba don al’ummu masu zuwa nan gaba.”

Kungiyar ta kuma nusar game da mamayar da jam’iyyun PDP da APC suka yiwa siyasar kasar nan, inda ta kara da cewa ‘yan Nigeria za su sami Karin dama idan aka samu wasu jam’iyyun masu karfi.

“Dattawan Arewa na hangen yanda za a sami tasowa da kuma haduwar wasu jam’iyyun a tafiyar siyasa. Cigaba da kasancewar hukumomin zabe na jihohi da ke gudanar da zaben kananan hukumomi na ruguza tsarin demokaradiya. Saboda haka Dattawan Arewa na bayar da shawarar cewa kokarin gyaran kundin tsarin mulkin Nigeria da ke gudana ya kamata ya kunshi rushe hukumomin zabe na jihohi da mayar da damar kula da zaben kananan hukumomi ga INEC.”

Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Nigeria, musamman ‘yan Arewa, da su yi rijistar katin zabe domin shirin gudanar da zaben shugabannin da suka cancanta a babban zaben shekarar 2023.

Comments
Loading...