Allah Ya yi wa babban malamin Addinin Musulunci nan na Kano Dr. Ahmad Ibrahim BUK, Kala Haddasana rasuwa a yau Juma’a.
Wata jikarsa ce ta tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Dr. Ahmad Ibrahim BUK ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.