For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dubban Faransawa Na Zanga-Zanga Kan Naɗin Sabon Firaminista

Dubban masu zanga-zanga sun fito kan tituna a sassan Ƙasar Faransa yau Asabar don yin watsi da nadin Michel Barnier a matsayin Firaminista da zargin shugaba Emmanuel Macron da karbar mulki ta ƙarfi.

Zanga-zangar ta gudana ne a birnin Paris da sauran birane irin su Nantes a yammacin kasar, Nice da Marseille a kudu, da Strasbourg a yankin gabas.

Macron ya nada Barnier, tsohon Ministan Harkokin Waje mai shekaru 73 wanda ya kasance mai shiga tsakani a shirin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, a matsayin Firaminista domin ci gaba bayan zabukan watan Yuli inda hadin gwiwar masu ra’ayin jarihujja suka rasa rinjayensu a majalisa.

Barnier ya bayyana cewa yana son nada ministoci daga bangarori daban-daban na siyasa, ciki har da wadanda ke da ra’ayin gurguzu.

Amma hadakar bangaren ƴan gurguzu, wadda ta zama karfin siyasa mafi girma a Faransa bayan zabukan, amma ba tare da rinjaye a majalisa ba, ta nuna rashin jin dadinta kan nadin Barnier.

A ranar Asabar, masu zanga-zanga da dama sun nuna fushinsu ga Macron tare da wasu da ke kira gare shi da ya yi murabus.

Shugaban bangaren gurguzu Jean-Luc Melenchon ya kira zaben da aka yi da cewa “an kwace shi daga hannun Faransawa” kuma ya bukaci jama’a su fito kan tituna don nuna rashin amincewa da nadin Barnier.

Comments
Loading...