‘Yan kwangilar gina tituna na bin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bashin kudin aiyukansu kimanin naira tiriliyan 11.16.
Ministan Aiyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a lokacin da kare kudirin kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2023, inda yai bayanin cewa, ma’aikatar tasa a yanzu haka ta bayar da kwangiloli 1,642 a manyan tituna na aiyuka 1,632 a kan kudi naira tiriliyan 10.395.
Fashola, wanda a lokacin da ya bayyana gaban ‘yan Majalissar Wakilai a Abuja ranar Talata ya samu uzurin “yi gaisuwa ka wuce” bayan kammala gabatar da bayanansa, ya bayyana cewa, “Babbar matsalar manyan tituna a kasa ita ce karancin kudade. A yanzu haka halin da ake ciki, ‘yan kwangila na bin gwamnati naira tiriliyan 10.4, da kuma kudaden takardun shaidar kammala aiki kimanin naira biliyan 765.
“Abu na biyu shine karancin kananan injiniyoyi a ma’aikatar, wanda ya samo asali daga takunkumin hana daukar ma’aikata da aka saka, hakan kuma na shafar aikin duba aiyuka. Muna tsammanin samar da hanyoyin samar da kudade da kuma janye takunkumin daukar ma’aikata domin akwai bukatar injiniyoyi da ma’aikatan gudanar da aiyuka a tsakiya domin duba aiyuka.”
A jawabin da ya gabatar, ministan ya ce, gwamnatinsu ta gina titituna masu tsawon kimanin kilomita 8,000 cikin tituna masu tsawon kilomita 13,000 da ake ginawa.