For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Duk Da Kalubale Ban Gajiya Wajen Cika Burin Matasan Mazabata Ba – Magaji Da’u Aliyu

Samar da Federal College of Education (Special), Birnin Kudu, Jihar Jigawa ya zama gagarumin abin farinciki ga al’ummar yankin gaba daya.

Engr. Magaji Da’u Aliyu, wanda yai sanadiyyar samuwar kwalejin, ya ce mutanen jihar Jigawa suna matukar godiya da nuna jin dadinsu game da abin da Majalissar Tarayya da Shugaban Kasa sukai musu na alkhairi ta hanyar sanywa dokar kwalejin hannu.

Ya bayyana hakan ne ga jaridar THE NATION a wata hira da tai da shi wadda TASKAR YANCI ta samu a shafin jaridar na yanar gizo.

Engr. Magaji, ya bayyana cewa, manufar samar da kwalejin shine, a karfafi harkar neman ilimi a matakin gaba da sikandire, kuma a yada shi ga kowa ba tare da nuna banbancin kabila, jinsi ko ra’ayin siyasa ba.

Dadin-dadawa, kwalejin za ta samar da damar koyar da karatuttuka na musamman da kuma amfani da kayan koyo da koyarwa daban-daban.

Engr. Magaji ya bayyana cewa, yunkurin neman kwalejin ya fara ne tun zamanin majalissa ta takwas, inda ta samu sanya hannu a wannan majalissar ta tara.

Engr. Magaji ya ce, “yunkurin neman wannan aiki ya fara ne a majalissa ta takwas. Duk da iya kokarin ganin an saya dokar hannun, kudirin dokar bai samu amincewar Shugaban Kasa ba a waccan majalissar.

“Ba tare da gajiyawa ba, mun sake ci gaba da neman a farkon majalissa ta tara. Mun shirya sosai, mun samu goyon bayan ‘yan’uwana ‘yan majalissa, wadanda suka jajirce a kan lamarin. Majalissar ta samu amincewa da kudirin a ranar 25 ga Fabarairu na shekarar 2021 inda ta mika shi ga Majalissar Dattawa wadda ita ma ta amince da shi a ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 2021.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya Ba Ta Mutunta Yarjejjeniyar Mu – ASUU

“Aikin majalissun yana karewa a kan kudirin, aka mika shi ga Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya sanya masa hannu a ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 2021 kuma aka aminta da tsarin gudanar da ita.

“Duk wadannan ba su kai ga nasara ba sai da aiki tukuru daga ‘yan’uwana ‘yan majalissa a Majalissar Wakilai da kuma ta Dattawa. Haka kuma, duk kokarinmu ba zai nasara ba, ba tare da amincewar Shugaban Kasa ga kiraye-kirayen al’ummar Jigawa kan bunkasa ilimi ba. Muna godiya ga kowa da kowa.”

Duk da matsalar da aka samu ta rashin nasarar kudirin a majalissa ta takwas, Engr. Magaji ya ce, “ba zan bar abun ya rushe ba, saboda wannan shine kiraye-kirayen da matasan mazabata suke ta yi. Tabbas ‘yan mazabata ba su raina temakon da muke bayarwa lokaci-lokaci ba kan bunkasa tattalin arzikinsu, amma ilimi shine gaba da komai a wajensu. Saboda haka, duk wata dama da matasa suka samu, abin da ke bakinsu shine su sami makarantar gaba da sikandire.

“’Yan mazabata sun san alfanun ilimi kuma suna samun matsalar samunsa a wannan zamani na gasesseniya a duniya. Shi yasa na kasa hutawa domin ganin burinsu ya cika a fannin ilimi. Kuma mun gode Allah, duk temakon da ake bukata daga ‘yan’uwana ‘yan Majalissar Tarayya, Kakakin Majalissa, Gbajabiamila da Shugaba Buhari ya samu.”

“Domin mu nuna muhimmancin wannan kwaleji gare mu, muna shirya gagarumin taron kaddamar da makarantar. Abun da kawai muke jira shine, umarni daga muhimman mutane da suka bayar da gudunmawa a tabbatuwar kwalejin. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya sa, Sarkin Kudu ya ziyarci Kakakin Majalissa.”

Comments
Loading...