For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ECOWAS Ta Yi Alkawarin Hada Kai Don Tabbatar Da Yin Zabe Cikin Lumana Da Adalci A Najeriya

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta yi alkawarin hada kai da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Najeriya, domin ganin an gudanar da babban zaben kasar na watan Fabrairun shekarar 2023 cikin lumana da adalci.

Sanarwar da hukumar ta ECOWAS ta fitar jiya Laraba ta bayyana cewa, tsarin rigakafin aukuwar rikice-rikicen na ECOWAS, wata manuniya ce ta jajircewa da fifikon kungiyar, na yin amfani da tattaunawa da shiga tsakani wajen warware takaddamar zabe da tashe-tashen hankula a shiyyar.

CRI Hausa

Comments
Loading...