For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

EFCC Ta Gano Ƙarin Naira Biliyan 90 Da Babban Akawunta Na Ƙasa Ya Wawura

Fadin binciken da Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa da Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC ke gudanarwa kan dakataccen Babban Akawunta na Ƙasa, Ahmed Idris na ƙara girmama, inda yanzu kuɗaɗen da ake zargin ya wawure suka kai Naira Biliyan 170.

Ahmed Idris, wanda a daren jiya yake fafutukar samun beli, ya tona asirin wasu manyan muƙarraban gwamnati da suke da hannu a kan kuɗaɗen da ake magana.

Hukumar EFCC dai ta kama wani Babban Sakatare da hannu cikin wasu abubuwa da suke da alaƙa da badaƙalar.

Haka kuma, hukumar na sanya ido a kan wani minista wanda aka nuna cewa yana da hannu kan badaƙalar da ake zargin Ahmed Idris da aikatawa.

An gano cewa, Hukumar EFCC ta damƙe dakataccen Babban Akawunta na Ƙasar ne bayan ya bijerewa gaiyatarta har sau 80.

Bincike ya nuna cewa, jami’an EFCC sun yi babban kamu game da hada-hadar kuɗaɗe a ofishin Babban Akawuntan.

Binciken ya gano cewa, duk da da farko ana zargin Ahmed Idris ne da wawure Naira Biliyan 80, a yanzu sakamakon binciken ya nuna akwai wasu ƙarin Naira Biliyan 90 da ake zargin ya wawure.

Akwai dai alamun cewa, dakataccen Akawuntan ya yi alƙawarin mayar da wasu daga cikin kuɗaɗen zuwa asusun gwamnati.

Wata majiya mai ƙarfi da ta buƙaci a ɓoye sunanta, ta baiyana cewa, “Yanzu haka, Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa da tawagarsa sun samu gagarumin ci gaba a binciken.

“Wannan ita ce badaƙala mafi girma da mulkin Bawa ya gano.

“Binciken farko a yanzu haka, ya nuna cewa, dakataccen Babban Akawuntan zai fuskanci tuhuma ne ta Naira Biliyan 170. Masu bincike na ci gaba da bincikar aiyukansa na office.

“Tun da aka kamashi a ranar 16 ga watan Mayu, ya baiyana muhimman abubuwa da suka haɗa da wasu asusun banki da hada-hadar da ake zargi.”

Ahmed Idris ya kuma tona asiri tare da bayar da jerin sunayen wasu ma’aikatan gwamnati da ke da hannu a hada-hadar kuɗaɗe a ofishinsa.

Majiyar ta ce, “Sakamakon tona asirin da yai a lokacin bincikarsa, an gaiyaci wani Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya inda aka yi masa tambayoyi a makon da ya gabata.

“Yanzu haka an bayar da belin Babban Sakataren, inda aka taƙaita zirga-zirgarsa a iya cikin Abuja. Babban Sakataren ya bayar da bayanai masu muhimmanci ga waɗanda suka bincikeshi.

An kuma tona asirin wani minista kan badaƙalar.

Majiyar ta ce, “Zamu binciki gaskiyar ko ministan yana da hannu cikin badaƙalar ko kuma kawai wanda ake zargin na ƙoƙarin shafawa wasu kashin kaji ne.”

Sahihin bincike na Hukumar EFCC ya nuna cewa, Ahmed Idris ya wawure kuɗaɗen ne ta hanyar da ba ta dace ba ta yin amfani da danginsa da kuma abokansa, in ji majiyar.

Comments
Loading...