Hukumar EFCC ta damke Hafsat Ganduje, matar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan zargin cin hanci da rashawa da danta ya yi, kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito.
Kamun ya zo ‘yan makonni bayan gazawar ta na amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi.
Tun da farko dai hukumar ta gayyaci Matar Ganduje ta kai kanta hedikwatar EFCC a Abuja a ranar 13 ga watan Satumba.
Sai dai EFCC ta ce dan ba ta bayyana ba za ta kamo ta.
Majiyoyin da ke da alaka da ita daga baya sun ce ta yi balaguro zuwa Burtaniya a lokacin don halartar bikin kammala karatun ɗanta.
A yanzu haka masu binciken suna yiwa mata tambayoyi kan zarge -zargen da suka shafi zamba cikin aminci kan filaye a kan karar da danta, Abdualzeez Ganduje ya shigar.
Wani mutum, wanda ke da masaniyar kamun amma ya nemi jaridar PREMIUM TIMES ta sakaya sunansa, ya ce “an kama ta da yammacin jiya Litinin.”
Har yanzu dai matar ta Ganduje tana hedikwatar EFCC kamar yanda jaridar ta tabbatar da misalin ƙarfe 6 na safiyar Talatar nan.