For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Zamfara Kan Badaƙalar Ofishin Babban Akawunta Na Ƙasa

Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa da Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, ta damƙe tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari bisa zarginsa da hannu cikin badaƙalar kuɗaɗen da ake zargin dakataccen Babban Akawunta na Ƙasa, Ahmed Idris da wawura.

Abdulaziz Yari dai ya yi gwamna a jihar Zamfara ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2019.

Wani babban jami’i a Hukumar EFCC ya sanar da wakilin DAILY TRUST cewa, an damƙe Abdulaziz Yari ne jiya da yamma da misalin ƙarfe 5 lokacin yana gidansa da ke Abuja.

Babban jami’in ya ce, “Jami’anmu sun kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Anthony Yaro, shugaba kuma babban daraktan kamfanin Finex Professional bisa zarginsu da hannu cikin badaƙalar kuɗi Naira Biliyan 84 tare da tsohon Babban Akawunta na Ƙasa.”

Da aka tambaye shi ko za a saki Abdulaziz Yari a daren jiya, jami’in ya ce, “Har yanzu bincikenmu yana gudana. Sai ya temaka mana wajen gano tushen lamarin.”

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Abdulaziz Yari da sukai, sai dai ya ƙi yin ƙarin bayani a kai.

Comments
Loading...