Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC na yankin Lagos da Enugu sun kama wadanda ake zargi da damfara ta yanar gizo guda 33 a samame daban-daban da suka kai.
Sanarwar da Mai Magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya saki a ranar Talata ta baiyana cewa, mutane 17 daga cikin wadanda aka kama an kama su ne a Lagos yayin da aka kama mutane 16 a Enugu.
“Wadanda ake zargin da aka kama guda 17 a Lagos sune Adefila Ayobami Ezekiel, Anamene Somtochukwu, Nzeako Kosisochukwu Anthony, Afolabi Ayomide Henry, Olatona Ayodeji Ebenezer, Obioho Ikenna Raphael, Famolayo Femi Hammed, Mintah-Joshua Oluwafemi, Martins Victor Onuoha, Babatunde Haruna Oluwaseyi, Taiwo Bolaji Kehinde, Ibeakolam Goodluck, Onaolapo Iyanu Samuel, Jamiu Damilola Lawal, Adeyanju Fawaz, AdejideSamuel da kuma Obioho Obinna,” in ji sanarwar.
“An kama su ne a rukunin gidaje da ke yankin Ikota a Lagos biyo bayan samun bayanan sirrin da hukumar ta yi na zargin aikata aiyukan laifi a bangaren wadansu da ake zargi da amfani da komfuyuta ta hanyar da ba ta dace ba.
A lokacin da aka kama su, an same su da manyan motoci, kwamfiyutoci da wayoyi.
Su kuma wadanda ake zargi su su 16 an kama su a Enugu a yankin Premier Layout da ke Enugu.
“Wadanda ake zargin sune, Ovu Chimezie, Junior Gentle Pepple, Nwoye Paul, Ezeoke Chimelue, Innocent Kenechukwu, Tochukwu Igbonekwu, Chigozie Oguanya,Nwachukwu Daniel and Charles Duru Chibuzor. Sauran sune Anderson D. Ugochukwu, Chinedu Nwasu, Obiora Martin Ugonna, Nwabueze Chidindu, Nwabueze Samuel Nnaemeka, Okechukwu Collins D da kuma Nwabueze Benjamin Ikenna”.
Hukumar EFCC ta ce, binciken farko da aka gudanar da ke da alaka da su ya nuna cewa suna yin sojan gona, da kuma mallakar takardun bogi da kuma damfarar ‘yan kasashen waje.
Kayaiyakin da aka samu a wajen wadanda ake zargin sun hada da mota Lexus ES350 mai lamba EPE113 HB, Mercedes Benz E350 mai lamba RSH 201 BP, sai kuma wata Mercedes Benz mai lamba UWN 338 MP da kuma Toyota Camry mai lamba JRV 944 KL; da kuma wayoyi da komfuyutoci da dama.
Za a kai su kotu nan ba da dadewa ba, bayan an kammala bincike.
(CHANNELS TV)