Hukumar EFCC ta samu sahhalewar kotu don ƙwace gidaje da gine-gine 40 na tsohon mataimakin shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Ike Ekweremedu na tsawon wani lokaci domin ta gudanar da bincike.
Mai shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Abuja ne ya sahhale wa EFCC karbe gidajen a ranar Juma’a biyo bayan karar da ta shigar tana neman a ba ta damar karbe gidajen domin ta gudanar da bincike kan su.
Hukumar dai na zargin sanatan da mallakar kadarorin ta ‘haramtattun hanyoyi’ kamar halasta kudin haramun.

Hotunan gidajen da EFCC ta wallafa sun ƙunshi na Abuja da kuma Jihar Enugu, inda nan ce mahaifar sanatan.
Yanzu haka Ekweremadu na fuskantar shari’a a birnin Landon game da tuhumar yunkurin cire sassan jikin wani matashi da kuma yin safararsa zuwa Birtaniya ba bisa ka’ida ba.
An kama sanatan da matarsa a watan Yunin da ya gabata a Landon bisa zargin kai wani mai suna David Nwamini da zimmar cirar ƙodarsa don bai wa ‘yarsu wadda ba ta da lafiya.