For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

EFCC Ta Samu Nasarar Hukunce-Hukunce 2220 A 2021

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, ta samu nasarar hukunce-hukunce 2220 a ofisoshinta a shekarar 2021.

An samu wadannan alkaluma ne daga bibiyar nasarorin hukumar da akai na shekarar da ta gabata ta 2021, inda aka samu ofishin hukumar na Lagos shine wanda ya fi kowanne ofishi samun nasarorin hukunce-hukuncen inda ya ke da 481, sai kuma ofishin Ibadan da ke biye masa mai nasarori 324, sai ofishin Fatakwal mai nasarori 230.

Nasarorin da hukumar ta samu a shekarar 2021, ta kasance mafi girma tun kafuwar EFCC.

Kafin 2021, nasara mafi girma da hukumar ta samu ita ce ta shekarar 2019 wadda aka samu nasarar tuhume-tuhume 1280.

KU KARANTA: Buhari Ya Yi Alkawarin Hukunta Masu Daukar Ma’aikata Ba Bisa Ka’aida Ba

Wannan ya nuna nasarori 2220 da aka samu a shekarar 2021 sun haura na shekarar 2019 da kaso 127.5%.

Wani abun kuma shine, wadannan nasarori 2220 da aka samu sune kaso 98.49% na adadin laifuffukan da hukumar ta shigar da kara a kansu, inda ta samu rashin nasara a kwaya 34 kacal a shekarar.

Da yake yabawa kokarin hukumar, Shugaban Hukumar ta EFCC, Abdulrashid Bawa, ya yabawa ma’aikatan hukumar saboda jajircewarsu da kokarinsu duk da kalubalen da ake samu a kotuna.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, EFCC za ta ci gaba da zaburar da duk ma’aikatanta saboda samun nasarori a gaba ta hanyar ba su horo da kuma ‘yan tagomashi.

Comments
Loading...