Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa da Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, ta ce ta yi manyan kamuta ne kan kudade a shekarar 2021 daga Ofishin Shiyyarta na Lagos, sai kuma na Abuja inda babban ofishinta ya ke; daga nan kuma sai Ofishin Shiyyar Kaduna da na Port Harcourt.
Mujallar wata-wata ta yanar gizo da hukumar ke wallafawa mai suna EFCC Alert ta ce, a iya shekarar 2021, EFCC ta kwato naira biliyan 70.31, dala miliyan 9.28, pound dubu 21.5 da kuma wasu kudaden yanar gizo.
A Abuja kuma, EFCC ta samu nasarar kwato naira biliyan 67.24, dala miliyan 375.66 da kuma yuro 155,251.76.
Ma’aikatan ofishin hukumar na Kaduna kuma, sun kwato naira biliyan 3.33 da dala 13,685; sai bangaren Port Harcourt inda ta samu nasarar kwato naira biliyan 2.14 da dala 125,077; Ofishin Shiyya na Sokoto kuma, naira biliyan 1.92, dala 56,950 da yuro 4,075; sai Ofishin Shiyya na Kano inda aka samu nasarar kwato naira biliyan 1.78, dala 194,098 da sari miliyan 1.72.
Daga Ofishin Shiyyar Benin kuma, an samu nasarar kwato naira miliyan 972.05, dala 49,240 da yuro 735; sai na Enugu inda aka kwato naira miliyan768.2, dala 22,735 da kuma AED 50; a Ibadan kuma an kwato naira miliyan 325.52, dala 383,385, yuro 2,670, pound 995, dalar Canada 1,400, BTC 1.3 da kuma ZARI 900.
Kari a kan haka shine, a Ofishin Shiyya na Gombe, hukumar ta samu nasarar kwato naira miliyan 388.59 da dala 1,500; a na Uyo kuma naira miliyan 234 da dala 357,000; sai na Maiduguri kuma inda aka kwato naira miliyan 970.42, yayin da a na Makurdi aka kwato naira miliyan 121.35; sai kuma na karshe, wato Ofishin Shiyya na Ilorin inda hukumar EFCCn tai nasarar kwato naira miliyan 240.96 da kuma dala 7,161.
Hukumar ta nuna cewa, tun lokacin da aka kafata shekaru 19 da suka gabata, ta ci gaba da samun nasarar yin aiyukanta da kuma nunawa sauran jami’an tsaro hanyar bi.
“Babu wata hukuma ta gwamnati da ta bayar da gudunmawa wajen tabbatar da bin doka a Najeriya cikin shekaru 10 sama da wannan hukumar,” in ji Shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa.
Jimillar kudaden da hukumar ta kwato a shekarar 2021 sune naira biliyan 152,088,698,751.64; dala miliyan 386,220,202.84; pound miliyan 1,182,519.75; yoro dubu 156,246.76; Riyal na Saudiyya miliyan 1,723,310.00 da sauransu.