Kungiyar ‘Yan Middle Belt, MBF, a jiya Lahadi ta yi martani ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’I kan bidiyon da ake ta yadawa kwanan nan wanda aka ganshi yana bayanin dalilan da suka sa ya zabi dan takara Musulmi maimakon Kirista.
MBF, a wani jawabi da Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Dr. Isuwa Dogo ya saki a ranar Lahadi ya ce, Maganganun El-Rufa’i na nuna kiyayya ne ga Kiristoci, inda ya bayyana shi a matsayin dan siyasa mai hatsari wanda ya zama wajibi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya guda.
A bidiyon da ake korafi a kai, an dau El-Rufa’i yana fadawa wasu malaman Musulunci a dab ranarsa ta karshe a ofis da yaren Hausa cewa, “Me ya sa na dauki Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta zama mataimakiyata 2019? Ina gaya musu cewa, na daya, na tsaya na yi lissafi cewa, yawanci wadanda ba Musulmi ba ba su zaben jam’iyyarmu (APC). Yawanci. Saboda haka me yasa zan ba su mataimaki?
“Na yi lissafi zamu iya cin zaben ba tare da mun ba su ba, na daya kenan. Wannan siyasa ne, so kake ka ci zabe, kana neman mutanen da zasu zabe ka, mun tsaya mun duba tun aka fara demokaradiyya mun duba inda muke cin zabe da inda ba ma ci, mun yi wannan lissafi. A siyasance kenan. Amma na biyu abin da muka so mu nuna, kuma cikin shekara hudun nan alhamdulillahi mun nuna, shine, gwamnati wanda gwamna Musulmi ne, mataimakiyar gwamna Musulmi ne, SSG Musulmi, Cheif of Staff Musulmi, Kwamishinan Kudi Musulmi ba zai cuci Kirista ba a Kaduna.
“Kuma duk inda muka je muna gaya musu cewa eh, haka ne, duk saman gwamnatinmu eh Musulmi ne, amma akwai Kirista guda daya a Jihar Kaduna da zai fito ya ce an zalunshi ba a ba shi hakkinsa ba? Akwai gundumar da ba mu gyara makaranta ba? Akwai gundumar ba mu gyara asibiti ba? Akwai inda ba mu je mun yi hanyoyi ba? Akwai inda ba mu taimaki manoma ba ko sun zabe mu ko ba su zabe mu ba? Mun ba wa kowa hakkinsu. Of course, Kubau sun fi zabarmu, saboda haka zan je Kubau in dan kara musu wani abu, ko? Domin sun zabe mu. Saboda haka abin da zan ba wa Jaba zan karawa Kubau tun da Jaba ba su zabe mu ba. Amma mun ba su hakkinsu.
A jawabinta, MBF ta ce, maganganun El-Rufa’i sun tabbatar da tsoron da ake da shi na Musuluntar da Najeriya.
MBF ta ce, “Babu makawa cewa wannnan tsohon gwamnan ya zama shaidar yanzu da kuma ta gaba cewa akwai matsalar rashin hadin kai a kasarmu. Yana aiki karara ga wasu masu fafutukar cusawa da kakaba fifikon addinin Musulunci a madafun shugabancin Najeriya.
“Da gwamna Uba Sani na Kaduna da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu dole ne su guji hada alaka da shi. Dole ne a hana shi kusantar madafun iko.”
Dadin da dawa, MBF ta yi kira ga hukumomin tsaro a kasa da cewar, “ba kawai su sanya ido a kan tsohon gwamnan ba, har ma da gayyatarsa da jami’an sirri zasu yi domin tattaunawa da shi.”