For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

El-Rufai Ya Warewa Ilimi Kaso 29% A Kudirin Kasafin Kudin Jihar Kaduna Na 2022

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gabatar da Kudirin Kasafin Kudi na Jihar na Shekarar 2021 ga Majalissar Dokoki ta jihar a Talatar nan.

Gwamnan ya gabatar da Kudirin Kasafin Kudin da ya kai Naira Biliyan 233 ga majalissar domin duba da tantancewa.

An yiwa kasafin take da ‘Kasafi don Samun Ingantaccen Cigaba’.

Gwamnan ya ce an ware Naira Biliyan 146 (kaso 63%) na kasafin domin manyan aiyuka da kuma Naira Biliyan 87.6 (kaso 37%) domin aiyukan yau da kullum.

Gwamnan ya ce, kasafin 2022 ya haura na 2021 wanda ya kasance Naira Biliyan 237.52.

Kamar sauran kasafin jihar na baya a lokacin gwamnatinsa, Gwamnan ya ce kasafin na 2022 zai fi mai da hankali wajen habbaka ilimi, lafiya da ababan more rayuwa.

An warewa bangaren ilimi Naira Biliyan 68.4 (kaso 29%) yayinda aka warewa bangaren lafiya Naira Biliyan 35.1 (kaso 15%).

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnantinsa za ta tabbatar da kammala dukkan aiyukan da ta fara kafin karewar wa’adinsa.

Comments
Loading...