For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Elon Musk Zai Nada Kansa Shugaban Kamfanin Twitter

Elon Musk ya bayyana cewa shi ne zai zama sabon shugaban kamfanin sada zumunta na Twitter wanda ya saya kan zunzurutun kuɗi dala biliyan arba’in da huɗu.

Ɗaya daga cikin matakan farko da ya ɗauka bayan kammala cinikin kamfanin, shi ne korar shugaban kamfanin wato Parag Agrawal.

Sai dai masu sharhi na ganin da wuya zai mayar da hankali wajen kula da kamfanin na Twitter duba da irin ayyukan da suka sha masa kai a kamfanoninsa na Tesla da Space – X.

Haka kuma Mista Musk ya rushe daraktocin kamfanin duk da cewa ya ce matakin na wucin gadi ne.

Ana ganin zai kawo tsare-tsare masu yawa kan yadda ake gudanar da kamfanin na Twitter ciki har da sauyi kan shafukan da aka tantance da shuɗin maki.

BBC Hausa

Comments
Loading...