For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ernest Shonekan, Tshohon Shugaban Rikon Kwarya A Najeriya Ya Rasu

Cif Ernest Shonekan, Tsohon Shugaban Rikon Kwarya a Najeriya wanda ya gaji shugaban mulkin soji, Janaral Ibrahim Babangida ya rasu.

Shonekan ya rasu ne a Lagos yana dan shekara 85, kamar yanda kafar TVC ta sanar.

Ernest Shonekan, ya yi jagoranci kwamitin rikon kwarya a Najeriya daga ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba na shekarar 1993.

An kawar da Ernest Shonekan ne daga mulkin Najeriya sakamakon juyin mulkin da Janaral Sani Abacha yai a shekarar, wanda kafin hakan, Abacha Sakataren Tsaro na Najeriya.

Comments
Loading...