Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace kasar zata gina sabbin cibiyoyin sarrafa mukamashin Nukiliya 14, duk fargabatar da ake da ita na kashe kudade mara kima. Shugaban wanda ke jawabi a wata cibiyar mukamashi dake gabashin kasar a ziyarar da yakai gabanin zaben shugabancin kasar dake tafe, ya buakci tsawaita cibiyoyin sarrafa mukamashin da ake dasu yanzu haka wadanda zasu iya kaiwa har shekaru 50 masu zuwa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana aniyarsa ta farfado da makamashin nukiliyar kasar, bayan da ya shirya samar da cibiyoyin sarrafa makamashin goma sha hudu da za su ba da damar sauya fasalin hanyoyin samar da man fetur da kuma lantarki.
Da yake la’akari da cewa Faransa ta yi jinkiri kan ko za ta ci gaba da saka hannun jari a bangarenta na nukiliya bayan bala’in da ya faru a Fukushima na kasar Japan cikin 2011, ya ce kasarsa ta shirya samar da sabbin fasahohin da za sua sauya fasalin bangaren nukiliyarta.
Hasken Rana
Kazalika shugaban ya nanata cewa dole ne a rubanya hannayen jari kan shirin makamashin hasken rana, iska mai kunshe da sinadarin hydrogen.
Samar da makamashin nukiliya mai araha ya kasance ginshikin tattalin arzikin Faransa tun cikin shekarun 1970, amma yunkurin gina cibiyoyin ya jefa kasashen Biritaniya da kuma Finland cikin rudanin karancin mai.
Masu fashin baki dai na ganin cewa sanarwar ta Macron ta yi daidai da sakamakon zaben shugaban kasa da za a yi a ranakun 10 da 24 ga Afrilu.
Galibin ‘yan takarar shugabancin kasar ta Faransa dai sun sha alwashin ci gaba da saka hannun jari a bangaren nukiliyar, in ban da dan takarar nan mai ra’ayin rikau Jean-Luc Melenchon.
(RFI Hausa)