A karon farko cikin shekaru 3, farashin danyen man fetur ya haura dala 80 kan kowace ganga a kasuwar man ta duniya.
Tun a ranar Talatar da ata gabata farashin man ya kai dala 80.69, abin da rabon da a gani tun watan Oktoban shekarar 2018.
Bayanai sun nuna cewa, farashin man ya yi ta hauhawa ne tsawon kwanaki bakwai da suka gabata, a yayin da kuma manazarta ke ganin cewa darajar ta sa, za ta ci gaba da karuwa sakamakon yadda bukatar danyen man ke karuwa a duniya, musamman la’akari da matakan da kasashe masu arzikinsa ke dauka na takaita adadin man da suke hakowa a kowace rana domin farfado da kimarsa.
In za a iya tunawa, farashin danyen man ya fadi warwas a farkon barkewar annobar Korona, inda a watan Afrilu na shekarar 2020, hada-hadar cinikinsa ta tsaya cak, karon farko a tarihi, biyo bayan matakan kullen da hukumomin kasashe suka dauka akan al’ummominsu, a daidai lokacin da kasashe masu arzikin danyen man na kungiyar OPEC da kawayensu basu dena hako shi ba.