For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Farashin Litar Fetur Zai Kai N410 Idan Aka Janye Tallafi – NNPC

Shugaban kamfanin man fetur na NNPC, Mele Kyari ya ce, farashin litar mai zai kai N410 kan kowanne lita guda, maimakon N170 da ake sayarwa a yanzu, da zarar an janye tallafin mai.

Kalaman Mele Kyari na zuwa ne kwana guda bayan an jiyo kungiyar dillalan mai ta kasa na cewa su na son a kai farashin man naira 200 zuwa 210 domin saukaka wahalhalun mai a faɗin kasar.

IPMAN ta ce janye tallafi ko karin kuɗin mai ne kawai mafita a wannan yanayi da Najeriya ke ciki.

Sai dai a lokacin da ya ke jawabi a gaban ‘yan majalisar wakilai, shugaban NNPC ya ce ana cikin wani yanayi saboda a halin yanzu cigaba da sayar da man kan naira 170 abu ne mai wahala, saboda farashin ya ninka haka sau uku.

Don haka dole ne wani ya rinka daukar asara, kuma yanayi ne da ba zai ɗore ba.

Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya.

Wannan ne ya sa farashin ya sauya a cikin watanni baya, abin da ya kawo sauki a wancan lokaci. Sai dai makonni bayan hakan sai wahalar ta sake kunno kai kuma har yanzu ana cikinta.

BBC Hausa

Comments
Loading...