For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Farouk Support Organisation Ta Yi Allah Wadai Da Yunkurin Hallaka Hon. Farouk Adamu Aliyu

Daga: Muhammed Sulaiman Ringim

A daren ranar Talata 28/04/2022 wasu gungun mahara da ake zargin ƴan aike ne ko sojojin haya sun yi yunkurin hallak Dan-Takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar APC Hon Farouk Adamu Aliyu a gidan sa dake Kano.

Wannan yunkuri ya zo ne dai-dai lokacin da aka fara hada-hadar siyasa ta kakar zaben shekara mai kamawa ta 2023.

A bisa wannan kungiyar Farouk Support Organization ke kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki musamman muhukuntan tsaro da su dauki kwakkwaran matakin tsaro domin kare lafiyar sa da ta iyalinsa tare da daukar matakin bincike domin gano masu hannu a cikin wannan aika-aikar.

A karshe muna qara godiya ga Allah bisa kare wannan bawa nasa da ya yi da kuma yin adduar kare afkuwar hakan a nan gaba. Muna qara kira ga masoya Honourable Farouk Adamu Aliyu da su kwantar da hankulansu tare da addu’o’in cigaba da samun kariyar Ubangiji.

Rubutawar: Muhammed Sulaiman Ringim
Shugaban Riko na Kungiyar

Comments
Loading...