Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani mutum daya sakamakon fashewar tunkuyar gas wadda ta faru a kauyen Ijarawa a Karamar Hukumar Bichi da ke jihar.
A jawabin da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar, wani mutum daya ya tsira a hatsarin.
Saminu ya ce, hatsarin ya faru ne a safiyar Talata wanda ya rutsa da mutane biyu; Wanda ya rasu, Maikano Muhammad dan shekara 45 da wanda aka cetar, Abdullahi Usman dan shekara 40.
“Mun samu kiran gaggawa daga Sufeta Daiyabu Tukur da karfe 7:46 na safe cewa, wata mota dauke da gas na girki ta yi hatsari kuma tukunyar gas daya ta yi bindiga.
“Muna samun wannan labarin, sai mukai sauri muka tura jami’anmu wajen 8:00 na safiyar domin su ceto wadanda abun ya rutsa da su.”
Ya kara da cewa, mota kirar J5 mai lamba FB 52 LAD wadda ta nufi Katsina daga Kano tana dauke gas na girki ce tai hatsarin.
“An mika dukkanin wadanda abin ya rutsa da su ga jami’in ‘yansanda, Usman Usman na rundunar ‘yansanda ta Bichi.
Ana cigaba da bincike kan musabbabin hatsarin.