For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Fayemi Bai Yi Katsalandan Kan Zaben Fidda Gwanin APC A Ekiti Ba, In Ji Gwamna Badaru

Kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar Ekiti, ‘yan takarar gwamna guda bakwai ne suka janye daga neman takarar, suna zargin cewa kwamitin shirya zaben ya shirya baiwa ‘yan takarar da Fayemi ke goyon baya ne kawai.

Da aka tambaye kan zargin magudin da aka tafka a yayin zaben fidda gwanin, Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce, babu ya isa ya sashi ya yarda da sakamakon da yake ba na gaskiya ba.

“Na ji zarge-zarge da yawa. Wadannan da ma ko yaushe sai an same su a siyasa saboda mutane za su yi tunanin abubuwa da dama, amma dukkanin ‘yan takara sun san babu wani a fadin kasar nan da ya isa ya sa ni na rubuta sakamakon da ba na gaskiya ba,” in shi.

“Ba zai yiwu kawai na zauna na rubuta sakamako ba. Babu wanda ya isa ya sa ni haka. Ba zan bar su su zo suna kalubalantar mu cewa kawai mun rubuta sakamako suna zargin ba ai zabe ba.

“Haka kuma, a zuciyar su (yana magana kan ‘yan takara bakwai da suka janye) ban hada kai da wani ba don na fitar da su.”

Da aka tambaye shi ko ya hada kai da Fayemi, Badaru ya ce, Gwamnan Ekiti ba zai ce masa ya yi ba dai-dai ba.

“A a. Ku tambayi Fayemi. Ko shi Fayemi ba zai ce min na yi ba dai-dai ba. Ba zai haka ba. Ya san ba zan yi ba,” in ji shi.

Gwamna Badaru ya kuma ce, an yi zaben fidda gwanin cikin gaskiya da gaskiya, inda ya kara da cewa, yana da shaidar hoton bidiyo wanda yake nuna ‘yan jam’iyya na yin zaben a lokacin zaben.

“Dukkanin mazabu cikin mazabu 166 da akai zaben, an yi shi cikin gaskiya da gaskiya, inda a ce ba ai dai-dai ba da an samu matsala, kuma da ya zama kamar yanda a ya faru a mazabu 11 da aka kawo matsala a cikinsu,” in ji Badaru.

Comments
Loading...