For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Fintiri Ya Yi Muhimmiyar Magana Kan Makomar Demokaraɗiyyar Najeriya

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nuna baƙin cikinsa kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo, inda ya bayyana cewa yana tausaya wa ga dimokaradiyyar Najeriya.

A ranar Lahadi ne hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba.

Fintiri ya bayyana wannan zaɓe a matsayin abin kunya da tsantsar rashin adalci ga tsarin dimokaraɗiyya.

Ya soki shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, bisa yanda ya shiga jihar ta jirgin saman kansa duk da hani da ƴansanda suka yi kan zirga-zirga.

Fintiri ya kuma yi zargin cewa sayen ƙuri’u da katsalandan a harkar tattara sakamako a kai a lokacin zaɓen, abin da ya haifar da samun ƙuri’u fiye da yawan masu rijista a jihar.

Ya ƙara da cewa, wannan ya tabbatar da cewa an ci mutuncin dimokaraɗiyya a Najeriya.

Fintiri ya ce, duk ƙoƙarin APC na ɓata masa suna ba zai kawar da ainihin almundahanar da aka tafka a yayin zaɓen ba, inda ya ce sakamakon da aka yaɗa a shafin nuna sakamakon zaɓe na Irev ya saɓa da abun da aka gabatar, abun da ya ce ya zubar da ƙimar demokaraɗiyya.

Comments
Loading...