Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sauka daga shugabancin jam’iyyarsa ta Conservative a jiya Alhamis.
Amma zai ci gaba da kasancewa firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.
Za a naɗa sabon shugaban jam’iyyar Conservative a wannan bazarar sannan za a yi sabon firaminista a watan Oktoba ɗin.
Boris Johnson ya gabatar da jawabin yin murabus ɗin nasa a gaban fadar No 10 Dawning Street.
Tun kafin ya kammala yin murabus ɗin a hukumance, har an fara kamfe kan wanda zai gaje shi.
Gabanin yin bayanin murabus din a hukumance an jiyo wani mai magana da yawun fadar Gida Mai Lamba 10 ya ce: “Firaministan zai yi sanarwa ga ƴan ƙasar zuwa an ji ma.”
Mr Johnson ya yi magana ne da Sir Graham Brady, shugaban kwamitin jam’iyyar Conservative na 1922 , inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka, a cewar wata majiya daga fadar No 10.
Majiyar ta ƙara da cewa: “Firaminsita ya yi magana da Graham Brady inda ya amince ya sauka a kan lokaci don ba da damar naɗa wani sabon shugaban a Oktoba.”
Me Boris Johnson Ya Ce A Jawabinsa?
Firaministan ya ce a yanzu ta bayyana cewa burin majalisar dokokin shi ne a samu sabon shugaban Jam’iyyar Conservative kafin a naɗa sabon firaminista.
Johnson ya ce a yanzu za a fara bin tsarin sabon shugaba kuma za a sanar da jadawalin hakan a mako mai zuwa.
“Na amince da abin da Sir Graham Brady ya ce, kan cewa yanzu za a fara shirin zabar sabon shugaba kuma za a sanar da jadawalin a mako mai zuwa.”
Johnson ya ci gaba da cewa ya fi ƙarfin a sauya shi a siyasa.
Tsarinmu mai kyau na zabar shugaba zai samar da wani sabon shugaban.
(BBC HAUSA)