For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Fitowar Dr. Nuruddeen a Matsayin Ɗan Takarar Sanata, Alheri Ne Ga Jihar Jigawa, Arewa Da Najeriya

Daga: Kabiru Zubairu

Tsarukan fedaraliyya da demokaraɗiyyar da muke ciki a ƙasar Najeriya, tsaruka ne da suke da buƙatar kyakkyawan duba da nazari wanda masana ko kuma gogaggun ‎‎ƴan siyasa zasu yi domin samun cikakkiyar nasara. Saboda haka ne, al’amarin yake buƙatar gudunmawar kowa, musamman kasancewarmu mabanbanta ƙabilu, addinai da yanayin yankuna.

A taƙaice, tsarukan sun zo da neman wakilai daga al’umma domin haɗuwa wajen tattaunawa da yanke hukunci kan yanda ake son kasa ta kasance. Wannan ne tsarin Najeriya kuma shi ake kai, saboda haka mai ƙafar gudu zai iya tserewa marar ƙafa a sikeli na kwatance.

A gaskiyance Majalissun Tarayyar Najeriya sun zama wajen ƙwatar ƴanci da kare kai, idan har wakilinka yana da ilimi, kishi da ƙwarewa to kasonka zai kasance mai tsoka, domin kuwa ba zai bari a cuceka ba. Akwai masu ƙorafin cewa gwamnati ta karkata akalar aiyukanta zuwa wani yanki da ba nasu ba – har ma wani lokaci zaka ji ana cewa, “Shugaban Ƙasar Yarabawa” ko wani abu makamancin haka. Hakan mai yiwuwa ne, musamman saboda jajircewar wakilan waɗanda ake ganin su ke morar gwamnatin da kuma gazawar wakilan waɗanda suke ganin hakan a kan su.

Har yanzu yankin Arewacin Najeriya yanki ne da a kullum ake masa kallon bakwauyen yanki, mai fama da marassa ilimi, talakawa da almajirai duk da kasancewar wasu alƙaluman zuƙi tamalle ce. A ƴan shekarun nan ana yi wa yankin kallon mai matasa marassa aikin yi, masu tayar da zaune tsaye da cin zalin waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. A kan irin wannan kallo da ake wa yankin, yankin kan rasa damarmaki na cigaba da samun kulawar gwamnatoci gaba ɗaya.

A Najeriyar gaba ɗaya ma, akwai abubuwan da suka zame mata ƙarfen ƙafa suka hana ta motsawa sai ma ƙara raunata ta da suke yi a kullum. Sa’annin Najeriya da ma ƙannenta da kuma waɗanda ake yiwa kallon yayunta ko iyayenta amma ba su damar da take da ita, sun yi mata fintinkau saboda wadatar tsare-tsaren ci gaba da kuma biyayya ga tsare-tsaren.

Duk da a Najeriyar ma akwai ƙwararru kuma masu bayar da gudunmawa, to amma kai wa abun ga zuciya da yi domin kishi ya hana ƙasar taɓuka komai na ci gaba. Babu yanda za ai Najeriya ta ci gaba har sai an samu, nagartattu kuma jajirtattu masu kishi da cikakken ilimin bukatu da kuma hanyoyin samun biyan bukatun.

Babu yanda za ai a dogara da mutum ɗaya ko mai kuwa girman nagartarsa, hanyar samun nasara kaɗai ita ce, a shugabancin ƙasa a samu nagartacce mai tsari, kishi da kuma yarda da ilimi, yayin da kuma a majalissu ake buƙatar cikakkun masana, masu kishi, masu ilimin matsaloli da kuma hanyar magance matsalolin sannan da jajircewa wajen iya tura buƙatarsu ta neman magance matsalar ko samar da maslahar da zata kai ƙasa ga samun ci gaba.

Da a ce duk jam’iyyu da sauran masu zaɓe, zasu tsayar su kuma zaɓi masu irin waccan nagarta, bisa kishi da amana, da an samu mafita daga tarun matsalolin da ke zame wa Najeriya ƙarfen ƙafa kuma suka hanata motsi.

Dr. Nuruddeen Muhammad shine manufata a wannan rubutu, a mu’amala ta da shi, da ɗan karamin nazari da nai a kansa, na gano cewa yana da abubuwan da ake buƙata domin samun cikakken wakilci a majalissar dokoki ta ƙasa, irin wakilcin da zai temaka wajen ɗora Najeriya a kan turbar samun cigaba.

Nura ɗan siyasa ne shi wanda bai kama da ‘yan siyasar da aka saba gani ba da jagaliyanci. Ɗan boko ne wanda bokonsa bai sa ya manta da al’ada da addininsa ba. Ɗan Jigawa ne wanda ya samu damar fita domin bayar da gudunmawa a wurare daban-daban na Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Dan Arewa ne kuma dan Najeriya wanda son yankinsa bai hana shi zama mai yin adalci ga kowa ba. Ina jin cewa, nagartarsa ba zata iya baiyyanuwa a rubutu guda ɗaya ba.

Dr. Nuruddeen ya yi karatu alhali idonsa da zuciyarsa suna buɗe, wanda hakan ya ba shi damar fuskantar hali da yanayin ƙasarsa, haka kuma jajirtacce ne musamman wajen zaƙulo mafita kan abun da ya hanga a matsayin matsala. Haka kuma tsayayye ne wajen ganin an tabbatar da biyayya ga tsarin da ake ganin shine dai-dai. Yana kallon komai da zuciyarsa, sannan yana kishin ganin matsala ta kau, ci gaba ya samu, hasali ma abun da ya ɗauka a matsayin neman ilimi shine neman hanyar temakon yayewa mutane matsala – kar a manta shi ƙwararren likita ne, likitan ma na ƙwaƙwalwa kafin shigarsa siyasar Najeriya ta dalilin ubansa Sule Lamido.

Dr. Nuruddeen ya yi aiki a matsayin likita tun bayan kammala karatunsa, ya zama ministan Najeriya mai riƙe da ma’aikatu har biyu, ya yi abin a zo a gani, har sai da ta kai Shugaban Ƙasa na wannan lokacin (Goodluck Jonathan) yana sanya shi a duk al’amuransa. Dr. Nuruddeen ya yi waɗannan aiyuka idonsa a bude, yana nazari tare da aiwatar da sauƙe nauyin da aka ɗora masa cikin ƙwarewa da gaskiya.

Waɗannan aiyuka da wasu da ba zasu bayyanu ba sun ƙara masa zurfin ƙara sanin yanayin Najeriya da kuma buƙatun da take da su, sannan dalilin waɗannan aiyuka, ya gano hanyoyi da dama da idan Najeriya ta hau kai zata samu ci gaban da ake bukata.

Nuruddeen Muhammad yana da biyayya da kuma tarbiyyar girmama manya da tausayawa ƙanana da marassa ƙarfi; wannan tasa ya buɗe gidauniyar Unik Impact Foundation. Ya koyi abun da ya koya na siyasa ne a wajen ubangidansa, Sule Lamido, wanda sananne ne a Najeriya a fannin siyasa da gwagwarmayar ƙwatawa talaka haƙƙinsa da kuma kare demokaradiyya. Wannan ilimi ne da kuma tarbiya da ake buƙata domin wucewa gaba wajen samawa al’umma mafita.

Dr. Nuruddeen yana da kawaici wanda har wasu ke masa kallon kamar ba ya son shiga siyasa, sannan yana da haƙuri da ƙasƙantar da kai wanda suke sa shi ture bukatun mutane na ya yi takara ko ya wuce musu gaba a wani lamari na rayuwa. Yana kyautatawa mutane zato, wanda hakan yake sa shi jin cewa abun da ake cewa ya yi wasu ma zasu iya. Amma kuma ba shi da gandar da zata sa ya yi wasarere da duk damar da aka ba shi.

Tabbas duk tsarin mutum da tunaninsa dole dai shi ɗin mutum ne, wanda Hausawa kan ce tara yake bai cika goma ba. Haka zalika, kowanne mutum yana da ƙaddararsa daga Allah SWT da kuma lokacin da zata same shi cikin yanayin daɗi ko akasin haka.

Mutane da yawa sun buƙaci Dr. Nuruddeen ya tsaya takarar neman Sanatan Jigawa ta Gabas amma ya turje ya ce ba ya buƙata, a ganina ya yi kuskure gaskiya kuma ya ɗau hanyar sauƙa daga kan halayyar da aka san shi da ita ta fifita buƙatar al’umma a kan tasa.

A haƙiƙanin gaskiya, ba buƙatarsa ba ce takarar sanata, buƙatar al’umma ce saboda yarda da kuma kyautata zato da suke masa kamar yadda a kayi a mukamai daban-daban a baya. Ina ganin babu abin da zai yi ya ci gaba da ɗora mutane a kan tarbiyyarsa da ya koya a wajen mai gidansa Sule Lamido kamar ya fito ya amsa kiran mutane ya tsaya takarar sanatan yankin Hadejia. Idan har zai tsaya a kan abun da aka san shi da shi, kuma ina kyautata zaton hakan, to tabbas ZAMEWAR DR. NURUDDEEN SANATA, ALHERI NE GA JIGAWA, AREWA DA NAJERIYA.

Kabiru Zubairu ya rubuto daga Birnin Kudu, Jihar Jigawa

Comments
Loading...