For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

FMC Birnin Kudu Zai Kulla Alakar Aiki Da FUD

Daga: Kabiru Zubairu

Sabon Shugaban Asibitin Gwamnatin Tarayya na Birnin Kudu, Federal Medical Center, FMC, Birnin Kudu, Dr. Abdullahi Adamu Atterwahmei ya yi kiran samun hadin guiwa tsakanin FMC, Birnin Kudu da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse, Federal Univerity Dutse wajen cigaban karatuttukan lafiya da danginsu.

Atterwahmie ya bayyana hakanne a lokacin da ya jagoranci jagororin asibitin zuwa wajen Shugaban FUD, Prof. Abdulkarim Sabo Muhammad.

Atterwahmie ya bayyana cewa, asibitin yana da kwararrun likitoci a fannoni daban-daban guda 30, da kwararrun ma’aikatan jiyya, masana magani da kuma kwararrun masu gwaje-gwaje wadanda za su temakawa sashin koyon ilimin lafiya na jami’ar.

KU KARANTA: Shugaban FMC Birnin Kudu, Atterwahmie Ya Gana Da Al’ummar Birnin Kudu

Atterwahmie ya bayyana cewa, kafin zuwansa FMC Birnin Kudu, lokacin yana FMC Nguru, an samu yarjejjeniya tsakanin asibitin da Jami’ar inda kwararrun likitoci 40 suka yarda su temakawa jami’ar a fannin ilimin lafiya.

Shugaban FMC Birnin Kudu ya kuma ce, ya riga ya tuntubi ma’aikatansa kan wannan hadinkan, inda ya bayyana musu irin amfanin da alakar za ta samar ga asibitin da kuma jami’ar.

Atterwahmie ya kuma taya Shugaban Jami’ar murna kan aiyana jami’ar da akai a matsayin jami’ar gwamnatin tarayya mafi inganci a yankin Arewa maso Yamma.

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar ta FUD, Prof. Abdulkarim Sabo Muhammad, ya taya shugaban asibitin murna kan nadinsa da akai a matsayin shugaban asibitin, tare da yi masa addu’ar fatan Allah yai masa jagoranci.

Ya kuma bayyana jin dadinsa da bukatar hada alaka da jami’ar, inda ya ce kwarewar ma’aikatan asibitin za ta temaka matuka wajen cigaban jami’ar.

Ya kara da cewa, jami’ar ta aminta da cewa, dole ne ma’aikatun gwamnatin tarayyar guda biyu su yi aiki tare domin cigaban ilimin fannin lafiya na jami’ar da ma al’ummar jihar gaba daya.

Prof. Abdulkarim ya bayyana cewa, kwanan nan Ministan Lafiya zai ziyarci jihar Jigawa domin aiwatar da mika asibitin ga jami’ar, inda ya ce hakan yana kammala, FUD za ta zauna da FMC, Birnin Kudu domin duba yanda za a tabbatar da kudirin shugaban asibitin na kulla alaka.

Comments
Loading...