Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, FUD ta kara bude damar cike neman gurbin karatu ga wadanda suke da sha’awar shiga jami’ar.
Rijistaran Jami’ar FUD, Abubakar Mijinyawa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya saki jiya Laraba.
Mijinyawa ya baiyana cewa, jami’ar ta dau wannan mataki ne saboda halin yajin aikin ASUU da ake ciki, inda yanke shawarar baiwa masu sha’awar damar nuna sha’awarsu domin samun gurbin karatu a jami’ar.

Wannan zai baiwa wadanda ba su sami damar yin rijistar a baya ba damar yi a yanzu.
An bude shafin cikewar (portal) na FUD tun daga ranar 2 zuwa ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2022.
Masu sha’awar cikewar kuma wadanda suka cika ka’idojin shiga jami’ar FUD za su iya ziyartar shafin cikewar idan suka danna kasa: