Ayarin motocin Dan Majalissar Wakilai mai wakiltar Birnin Kudu/Buji a jihar Jigawa, Magaji Da’u na jam’iyyar APC ya fuskanci fushin wasu ‘yan mazabarsa bayan sun zarge shi da rashin yin wakilci na gari.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, al’amarin ya faru ne a lokacin da dan majalissar ke kan hanyarsa ta zuwa Kukuma taron siyasa, inda fusatattun suka tare hanyar.
Mutane suna kalubalantar dan majalissar ne bisa rashin wakilci na gari tare da yin watsi da ‘yan mazabarsa, sai ‘yan kwanakin nan inda yake nuna kansa saboda kuratowar zaben shekarar 2023.
Lamarin ya jawo hatsaniya tsakanin fusatattun mutanen da magoya bayan dan majalissar da ke ayarin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ‘yansanda na jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya ce an farmaki dan Majalissa Magaji Da’u ne a kan hanyarsa ta zuwa wani taron siyasa.
“An shawo kan lamarin, kuma ‘yansanda sun kama wadansu daga wadanda ake zargi da tayar da hatsaniyar,” in Lawan Shiisu.
TASKAR YANCI ta tuntubi wani magoyin bayan Magaji Da’u kan lamarin, inda ya bayyana cewa, tabbas lamarin ya faru, amma wadanda suka kai harin ba suna zargin dan majalissar da rashin iya wakilci ba ne, sai dai wadanda dan majalissar ya sanya su zama wakilansa a yankin karamar hukumar Buji ne ba sa yi musu yanda ya kamata.