For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ganduje Ya Mayar Da Martani Bayan Kotu Ta Soke Shugabannin APC Na Tsaginsa

Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ta soke zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Kano.

Bangarori biyu masu hamayya da juna na APC a jihar sun gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar mabanbanta a jihar a ranar 18 ga watan Oktoban da ya gabata, sai dai bayan nan babban ofishin jam’iyyar ta kasa ya amince da bangaren gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Daya bangaren wanda Sanata Shekarau ke jagoranta ya zabi Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kanon yayin da bangaren Gwamna Ganduje suka zabi Abdullahi Abbas.

Kwamitin da jam’iyyar APC ta kasa ta kafa, daga baya ya bayyana Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.

Bangaren Shekarau sun nuna kin amincewa da hukunci inda suka garzaya kotu, suna bukatar kotun da ta soke zaben da aka gudanar tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi da matakin jiha na bangaren Ganduje tare da amincewa da wanda bangaren Shekarau suka gabatar.

Da yake gabatar da hukuncin, Alkali Hamza Muazu, ya amince da bukatar inda ya tabbatar da zaben shugabannin da bangaren Shekarau suka gabatar a jihar.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin dakatar da bangaren Ganduje daga bayyana kai a matsayin shugabannin jam’iyyar.

Da yake mayar da martani bayan yanke hukuncin, bangaren Gwamna Ganduje ta bakin kwamishinan shari’a na jihar, Alkali Musa Lawan, ya bayyana cewa za su daukaka kara kan hukuncin.

Alakali Musa ya ce gwamnatin Kano na nazarin hukuncin kafin yanke hukuncin abin da za tai a gaba.

“Muna nazarin hukuncin, muna so mu ga ko kotun na da hurumin saurarar karar,” in ji shi.

Comments
Loading...