For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ganduje Ya Shirya Karɓar Kwankwaso A APC, Ya Ce Kyakkyawan Ɗan Siyasa Ne

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana shirinsa na karɓar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso matuƙar ya yarda ya shiga jam’iyyar.

Ganduje ya yi wannan magana ne a lokacin da yake tattaunawa da wasu ƴan jarida a Kano.

Ganduje ya ce, “Babu wanda zai ce ba ƙwararren ɗan siyasa ba ne, a ƙalla dai ya zama gwamnan Kano na wa’adi biyu, duk da dai a tsittsinke ne, ya zama Ministan Tsaro, duk da dai bai san mene ne tsaron ba, sannan kuma ya taɓa zama sanata, duk da dai bai ce komai ba tsawon lokacin da ya ɗebe a can.

“Amma, idan har yana so ya komo APC, ƙofarmu a buɗe take, musamman ma a yanzu da wani daga jiharsa yake shugaban jam’iyya, zai masa sauƙi ya roƙi a karɓe shi.”

Lokacin da aka tambayi Ganduje ko mene ne dalilin da ya sa ba a sa sunan Kwankwaso a cikin sunayen ministocin Tinubu ba, Ganduje ya ce, da ma ba a yi wa Kwankwaso alƙawarin hakan ba tun a farko.

Ganduje ya ce, da ma a wajen Kwankwason ya ji wannan maganar, lokacin da ya dawo daga ganawar da yai da Shugaban Ƙasa a birnin Paris na Faransa.

“Eh gaskiya ne, Shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin yin gwamnatin haɗin kai, kuma ya cika alƙawarinsa. Nyesom Wike ɗan PDP ne, kuma yanzu an miƙa sunansa za ai masa minista. Amma shi (Kwankwaso), shi ne ya ce za a ba shi muƙami tun farko, amma ba Shugaban Ƙasa ne ya faɗa ba,” in ji shi.

Tattaunawa da ƴan jaridu na farkon da yai, na zuwa ne kwanaki huɗu bayan an naɗa shi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa a taron jam’iyyar da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Comments
Loading...