Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin cewa zai amfani da damarsa ta kundin tsarin mulki wajen sanya hannu a hukuncin kisa idan har kotu ta zartar da hakan, a kan wadanda sukaiwa yarinyar ‘yar shekara biyar ta’addanci mai suna Hanifa Abubakar Abba.
Gwamnan ya bayyana hakanne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyayen marigayiyar da ke zaune a unguwar Dakata/Kawaji a yau Litinin.
A lokacin ziyarar, Gwamna Ganduje yana tare da Mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Shugaban Masu Rinjaye na Majalissar Dokokin Jihar Kano, Labaran Abdul Madari da sauran manyan mukarraban gwamnati.
“Muna da tabbaci daga kotu cewa za a tabbatar da an yi adalci. Babu wani abu da za a bari a rufe,” in ji gwamna.
KU KARANTA: Wani Ya Kashe ‘Yar Makwabcinsa ‘Yar Shekara 8 Bayan Ya Karbi Kudin Fansa Milyan Uku
Gwamnan ya tabbatar da cewa, “Duk wanda aka samu da laifi na wannan ta’addanci zai fuskanci hukuncin kisa ba tare da jinkiri ba. A matsayinmu na gwamnati mun riga mun fara shirin hakan.”
Ya kara da cewa, “Kundin Tsarin Mulkinmu ya ce, duk lokacin da aka yanke hukuncin kisa, damar gwamna ne ya sanya hannu domin tabbatar da hukuncin kan wanda yai laifin. Na tabbatar muku duk dinku, ba zan bata sakan daya ba wajen amincewa.”
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa za a gaggauta yin adalci kan shari’ar inda ya kara da cewa, “Gwamnati za ta bayar da kulawa ta musamman ga iyalan ‘yarmu marigayiya Hanifa.”
Game da makarantun da al’amarin ya shafa, gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnati za tai abun da ya kamata game da makarantun.