For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Garin Saka Caji, Lantarki Ta Ja Wata Mata ‘Yar 36 Har Lahira A Taraba

Wata mata ‘yar shekara 36 ta mutu a dalilin jan da wutar lantarki tai mata a garin Jalingo na Jihar Taraba.

Matar, wadda aka bayyana sunanta da Jindori Ignatius ‘yar kabilar Kona, ta mutu ne a lokacin da kake kokarin sanya cajin wayarta lokacin da aka kawo wuta a yankin da take.

Rahotanni sun bayyana cewa, hannunta, cajar wayar, da kuma wayar duk sun kone a lokacin.

Hatsarin ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata da yamma a yankin Nukkai da ke Jalingo, bayan cocin Arrow of Deliverance Church.

Wani danuwan marigayiyar, John Ignatius ya bayyana cewa, yankinsu ya dade yana fama da matsalar yanayin kawo wutar kusan watanni hudu ba tare da an gyara musu ba.

Comments
Loading...