For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gazawar APC Na Magance Rigingimun Ta A 2021 Kan Iya Yi Mata Sartse A Zaben 2023

Daga: Comrade Ahmed Ilallah

Kasa da wata 13 ga zaben kasa na 2023, shin watanni 18 na jagorancin Mai Mala Buni, ya shirya wa APC tinkarar wannan zabe?

Ire-iren rigingimun da suka addabi APC tun bayan samun nasarar ta a 2015, ya janyo ficewar manyan yan siyasa irin su tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da makamantansu.

Tun bayan cire Adams Ohomole da Kotu tayi daga shugabancin APC, biyo bayan korar da Jama’iyar APC daga Ward din sa  tayi masa, bisa rigimar sa da gwamnan Jahar san a Edo. APC ta shiga cikin rikici na shugaban cin, kafin samun matsaya na kafa kwamitin Mai Mala Buni. Yanzu kima nin shekara daya da rabi Kenan da rushe shugabancin jama’iyar APC bisa jagorancin Comrade Adams Oshomole.

A ranar 25/6/2020 aka nada Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, wanda yake tsohon sakatare APC ne na kasa har sau biyu, don ya jagoranci Jama’iyyar APC, karkashin kwamatin da aka kira Caretaker/Extraordinary Convention Planning Committee (CECPC). Kuma Mai Mala Buni yayi alwashin yin adalchi ga duk yan jama’iyya don magance rigingimun dake cikin jam’aiyar.

Mai Mala Buni yana samun goyon bayan Shugaba Buhari da yan uwansa a Gwamnonin APC, hakkan yasa  ake karawa wannnan kwamitti lokacin don shawo kan rigingimun da ke faruwa a jama’iyyar, a wani bangagren kuma yana samun suka, musamman da ga wasu jagororin jama’iyyar.

Koda a wannan kwanakin sai da wata kungiya maisuna Progressive Youth Movement (PYM) bisa jagorancin Prince Mustapha Audu, ta fito ta sanar da cewa to tsige Mai Mala Buni da CECPC, kuma ya tabbatar da Mr. Prince Mustapha Audu a matsayin sabon shugaban Kwamitin da zai jagoranci APC, bisa zargin sa da kin yin abin da ya dace wajen sasanto ga yan jama’iyyar daga wajen su Mai Mala Buni.

PYM ta kafa kwamitin ta na sasanto karkashin jagorancin Mr.  Hassan Saddiq Arivi, ta sanya ranar 26/2/2022 a matsayin ranar da za ta gudanar da babban taron APC na kasa.

Wata kungiya har ila yau ta sake billa karkashin APC wato APC Rebirth Group, bisa jagorancin Mr. Aliyu Audu, suma sun soki rashin iya gudarwar wannnan kwamitti, wanda suka ce har ma gwada lokacin Adams Oshomole da wannan lokacin.

CECPC bisa jagorancin Mai Mala Buni ta ci karo da wasu matsalolin daban daban, kama daga sabinta katin jama’iyya, zaben shugabanni daga mazabu, kananan hukumomi zuwa jaha.

Rigingimun zaben fidda gwani (Primary Election) a wasu jahohin a 2019, APC tayi asarar kujerun gwamnonin Bauchi, Zamfara, Adamawa da Edo, duk da kasancewar ta samu shigowar was gwamnoni cikin ta, kamar gwamnan Cross-Rivers da Zamfara.

Ana magani kaba kayi na kumbura, kamar abin da ke faruwa a Jahar Zamfara Kenan, ana murnar dawowar Gwamna Matawalle, sai gashi rigimar karuwa tayi akan ta baya tsakanin Gwamna Yari da Senator Dan Sadau, yanzu kuma ga Matawallle a wani tsagin.

CCEPC bisa yardewar shugaba Muhamadu Buhari da Gwamnonin APC sun sanya watan gobe na February 2022 don gudanar da babban taron APC na kasa, duk da ba fidda rana ba. Akwai kaluballe mai girma a kan CECPC na iya gudanar da babban taron jama’iyyar na kasa, da zai kawo karshen rikon kwaryar jama’iyyar, ya samar da shugabbanin da za su tunkari babban zaben kasa na 2023. 

Tarukan Jama’iyar APC na Jahohi, a yayin da aka zabi sabbin shugabbanin yabar baya da kura a akalla jahohi 20 da suka hada da Kano, Zamfara, Imo, Abia, Ogun, Oyom Ekiti, Osun, Lagos, Akwa Ibom, Cross Rivers, Adamawa, Enugu, Kwara, Anambra, Bauchi, Gombe, Niger suna cikin rikici daban-daban.

Wasu daga cikin waddan nan Jahohin sun garzaya kotu, har ma sun sami hukuncin da bai yi wa uwar jama’iyyar dadi ba, kamar a Jahar Kano tsakanin  Abdullahi Abas dake da goyon bayan Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da bangaren Haruna Danzago dake da goyon bayan tsohon  gwamnan Kano  Senator Ibrahim Shekarau dake da wasu yan majalissun tarrayya guda shida.

A arewa maso yamma, wurin da ake gani APC na da karfi bayan Arewacin Nijeriya, a Jihar Legas kadai Jamaiyyar APC ta kasu gida uku, Gidn tinubu da kuma yan kugiyar Lagos4Lagos Movement bisa jagorancin Dr. Abdul’azia Adediran, wanda suka yi tsokacin rashin iya gudanarwar Mai Mala ce ta jawo suka yi aware a zaben shugabannin jama’iyyar da ya gabata.

Senator Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan Jahar Nasarawa, yana Jagorantar kwamittin sasanto biyo bayan wannan zabubbuka, amma fa har yanzu wannan kwamitti bai iya shanwo kan yan jma’iyyar da suke rikici da juna a jahohi daban-daban ba.

Wucewar shekarar 2021 da tayi ba tare da Jama’iyyar APC ta iya shawo kan wadannan rigingimu ba, zai iya kawo wa jama’iyyar da tafi kowacce farin jini a shekarun baya chikas wajen tunkarar zaben 2023. Ganin har yanzu kwamittin jama’iyar ya kasa shawo kan yan jama’iyyar da suke rikici, CECPC ta kasa sanya ranar yin babban taron ta na kasa, gashi kuma za a tafi zaben primary election da babban zabe na kasa.

alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...