Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi kira da samar da Bankin Ilimi a Nigeria wanda zai samarwa daliban manyan makarantu bashi marar ruwa domin a samu gudanar da biyan kudin karatu ga kowa da kowa.
Gbajabiamila, ya kuma yi kira da asamar da Tsarin Baiwa Dalibai Bashi a kasar.
Kakakin ya yi wannan kira ne a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake jawabi taron kaddamar da dalibai karo na 52 na Jami’ar Lagos, UNILAG.
An yiwa jawabin Kakakin take da: Sake Ginawa da Inganci: Kirkirar Sabon Tsari Domin Karatu a Manyan Makarantun Najeriya a Karni na 21.
KU KARANTA: Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Badaru Kan Musabakar Al-Kur’ani
Kakakin ya bayyana cewa, a kan wannan batu, ya gabatar kudirin doka a Majalissar Tarayya mai taken: Bashi Domin Dalibai (Kudirin Doka Domin Samun Damar Yin Karatu a Manyan Makarantu).
Ya bayyana cewa a matsayinsa na dan majalissa kuma dan siyasa, daya daga cikin yawan bukatun da yake karba sune na biyan kudin karatu, saboda haka goben dalibai za ta iya kasancewa cikin matsala.
“Kudirin dokar an shirya shi ne domin samar da bashi marar ruwa ga dalibai. Biyan irin wadannan basussuka zai fara ne shekaru biyu bayan kammala aikin bautar kasa. Haka kuma, ya kamata duk mu fahimci cewa, gudunmawar al’umma a kan irin wannan tsari zai dogara ne ga manyan makarantu.
“Majalissar Wakilai ta Tara ta sanya ilimi a matsayin daya daga cikin bangarorin da ta fi baiwa muhimmanci a tsarinta. Alal misali, mun dauki matakin daukaka da yawa daga cikin makarantun gwamnati, daga darajar wasu kwalejojin ilimi zuwa jami’o’in ilimi da sauran abubauwa,” in ji shi.