For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gbajabiamila Ya Ki Karbar Shaidar Cin Zabe, Yana Jiran Mukami A Gwamnatin Tinubu

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, bai halarci inda aka gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababbun ‘yan Majalisar Wakilai, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi a ranar Laraba ba.

An sake zaben Gbajabiamila a matsayin wanda zai wakilci mazabarsa ta tarayya ta Surulere 1 a Jihar Legas a karo na shida a jere a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Ya samu kuri’u 19,717 inda ya doke abokin hamayyarsa Bosun Jeje na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 5,121.

Jaridar LEADERSHIP, ta gano cewa, shugaban majalisar ba zai wakilci mazabarsa a Majalisar Wakilai ta 10 ba saboda akwai yiwuwar za a bashi mukamin Shugaban Ma’aikata a gwamnatin Tinubu.

Wata majiya da ke kusa da Gbajabiamila ta shaida wa LEADERSHIP din cewa, Shugaban Majalisar, kasancewarsa daya daga cikin jiga-jigan masu goyon bayan Tinubu kuma ya yi aiki da ’yan siyasa daga kowace mazabar tarayya a Najeriya a cikin shekaru 20, ana son ba shi mukamin.

Da aka tuntubi mai bai wa kakakin majalisar, Gbajabiamila shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Mista Lanre Lasisi, ya tabbatar da cewa shugaban nasa bai samu damar halartar bikin ba da takardar ba ne saboda wani uzuri.

An fara zaben Gbajabiamila a matsayin dan majalisar wakilai a shekara 2003, wanda tun daga lokacin ne ya lashe zabe a zabuka biyar da suka biyo baya.

A tsawon shekaru 20 da ya yi a Majalisar Wakilai, Gbajabiamila ya rike mukamai irinsu Mai Kare Marasa Rinjaye, Shugaban Marasa Rinjaye, da kuma Shugaban Masu Rinjaye, kafin a zabe shi a matsayin Shugaban Majalisar a 2019.

LEADERSHIP

Comments
Loading...