Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar mata da miji da ‘ya’yansu biyu a Layin Dangan Waya, Rimaye a yankin Rimaye na Rigasa a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Hatsarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 11 na dare, lokacin da matar mai suna Zaliha da mijinta mai suna Musa da ‘ya’yansu guda hudu suna cikin bacci a daki.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa makwabta sun ceto ‘ya’ya biyu daga cikin ‘ya’ya hudu na marigayan bayan sun samu raunuka.
Wani makwabcin wadanda hatsarin ya shafa, wanda ya ce sunansa Suleiman ya ce, gobarar ta fara jim kadan bayan an dawo da wutar lantarki.
“Suna dawo da wutar lantarki da misalin karfe 11:00 na dare, na ji wata kakkarfar kara. Na yi tunanin transformermu ce ta yi karar, amma daga baya sai na ga hayaki na fitowa daga gidan makobcina.
“Mun yi kokarin kashe wutar, amma wutar ta riga ta mamaye dakin gaba daya. Mun samu nasarar ceton ‘ya’ya biyu, amma mahifin da mahaifiyar da wasu ‘ya’yansu biyu sun mutu a wutar,” in ji shi.
Hakimin Makera, Malam Isiaku Abdulwahab Umar ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce abun kaice no.
Tuni dai an riga an yiwa marigayan sutura kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.