For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Goodluck Jonathan Ba Ɗan APC Ba Ne, In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyyar

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, APC na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Muhammed Lukman ya ce, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ba ɗan jam’iyyar APC ba ne.

Salihu Lukman, ya baiyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilin jaridar PUNCH ta wayar salula a daidai lokacin da wasu rahotanni ke wasu daga cikin manyan jam’iyyar na neman tsayar da Jonathan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar.

Ya ce ya ɗauki labaran da ke ƙoƙarin janyo Jonathan a matsayin tsokanar jam’iyya da kuma abin takaici.

Ya ce, “Zan iya faɗa maka wannan kai tsaye, a wajen jam’iyyarmu, Jonathan ba ɗan jam’iyyar APC ba ne. Abubuwan da ake tattaunawa a kafafan yaɗa labarai, abin mamaki ne ga mafi yawanmu. Ba mu san cewa wani ya siyawa Jonathan fom ɗin tsayawa takara ba, kuma mun riga mun rufe siyar da fom.

“Duk waɗannan suratan da ake kafafan yaɗa labarai, duk da dai mun san komai me iya faruwa ne a ƙasar nan, amma a tsarin jam’iyyar mu, kuma wasun mu suna riƙe da muhimman gurabe a jam’iyyar, wannan ba zai taɓa faruwa ba.

“Za ka iya kafa hujja a kaina cewar na ce, wannan ba zai taɓa yiwuwa ba. Duk mai yin wannan maganar kawai yana shirme ne.”

Da aka ce masa akwai waɗansu manya a jam’iyyar APC da ke son takarar Jonathan a APC, Salihu Lukman ya ce shi bai san da wannan ba.

“Ban san wani ba, Shugaban Jamiyya ko mamba a Kwamitin Shugabancin Jam’iyya da ya yi irin wannan magana ba. Amma duk inda aka jiyo wannan magana, to an yi ta ne a bisa kuskure. Hakan ba zai yiwu ba.

“Jonathan ma ba ɗan APC ba ne a sanin mu. Bayan haka, kasancewa ɗan jam’iyyarmu ba abun ɓoyewa ba ne. Ka ce na ce haka a ko’ina,” in ji shi.

Lukman ya soki rahotannin da ke cewa APC zata yi amfani da sasanto wajen fitar ɗan takarar Shugaban Ƙasa, inda ya ce, APC zata bai wa kowa dama.

Yunƙurin da akai na tuntuɓar ɓangaren Goodluck Jonathan kafin haɗa wannan rahoton ya ci tura.

Comments
Loading...