For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Goodluck Jonathan Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu A Villa

A jiya Juma’a, tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya ziyarci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce, tun da harkokin zaɓe sun zo ƙarshe, ya kamata tsofin shugabanni da masu ci a yanzu da ma masu yin zaɓe su haɗu su yi aiki tare domin samun kyakkyawar gobe ga ƙasa.

Jonathan ya tabbatar da cewar akwai matsalolin tattalin arziƙi a Najeriya, amma kuma duk da haka Najeriya na da ƙarfin da za ta iya jagorantar Nahiyar Afirka.

Tsohon shugaban ƙasar dai ya bayyana hakan ne ga manema labarai da ke Fadar Shugaban Ƙasa bayan fitowarsa daga ganawar sirri da suka yi da Shugaba Bola Tinubu.

Da yake magana kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Alhamis, Jonathan ya ce, akwai buƙatar a haɗa kan jagororin siyasa, domin idan aka ƙayale su suka ci gaba da faɗa, na ƙasa ne za su sha wahala.

Comments
Loading...