For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

GURBIN AIKI: Neman Aikin Internship A NNPC Da Seplat Energy Ga Masu Karatun Degree

Kamfanin Seplat Energy Nigeria ya bude damar neman aikin internship ga wadanda suke karatun digiri ‘yan Najeriya.

Kamfanin Seplat Energy Internship ta shirya tsaf domin samarwa dalibai damar samun aiki ta hanyar ba su damar dabbaka iliminsu inda zasu samu cikakkiyar kwarewa da gogewa a fannin masana’antun makamashi (energy).

Masu samun kwarewar zasu shiga cikin aiyuka tare da kwararru da kuma samun damar kulla alaka da shaharrarun kwararru a fannin.

Wannan dama ce ga daliban jami’a, wadanda suka kammala akalla shekarar farko ta karatun degree, haka kuma, tsawon lokacin samun kwarewar zai kama watanni 3, 6 ko 12.

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Samun Damar

Domin samun wannan damar a Seplat Energy, dole ne mai nema ya cika wadannan ka’idar gabatar da takardar neman amincewa don yin SIWES wadda HOD nasa ya rubuta zuwa SEPLAT HR, haka kuma za a tuntubi wadanda suka cika dukkan ka’idoji ne domin gayyatarsu zuwa aikin neman kwarewar.

Wadanda suka cika ka’idojin zasu kuma cike form na neman aikin idan suka danna nan.

Comments
Loading...