For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gurfanar Da Masu Zanga-Zangar #EndBadGovernance Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyya — NANS

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta bayyana damuwarta game da gurfanar da mutanen da suka shiga zanga-zangar #EndBadGovernance.

Ƙungiyar ɗaliban ta bayyana matakin shari’a da aka ɗauka a matsayin babbar barazana ga dimokuradiyya a Najeriya.

NANS ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sa baki don dakatar da gurfanar da masu zanga-zangar, tare da jaddada muhimmancin kare haƙƙin yin zanga-zangar lumana da ƴancin faɗin albarkacin baki.

Wannan yana cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar, Akinteye Babatunde, ya fitar a yau Talata.

Babatunde ya ce irin waɗannan shari’u sun saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya da Najeriya ke alfahari da su.

NANS ta yi nuni da cewa masu zanga-zangar sun fito kan titi ba da mugun hali ba, amma sai don cikakken burin kawo sauyi mai kyau a ƙasa.

Kungiyar ɗaliban ta yi kira ga gwamnati da ta shiga tattaunawa mai ma’ana da ƴan kasa domin warware matsalolin da ake ciki cikin lumana.

Ta kuma yi gargaɗin cewa cigaba da gurfanar da waɗannan mutane na iya haifar da yanayin da zai na hana ƴan ƙasa shiga cikin lamuran da suka shafe su da kuma takura wa bayyana ra’ayi a tsarin dimokuradiyya.

A ranar Litinin ne, Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da masu zanga-zangar #EndBadGovernance guda 10 da aka kama a Abuja, Kaduna, Kano, da Gombe a gaban Babbar Kotun Tarayya.

Ana tuhumar waɗanda aka kaman da laifuka guda shida, ciki har da zargin cin amanar ƙasa, yunkurin tada zaune tsaye a Najeriya, haɗin baki don aikata laifi, da kuma ƙoƙarin tada bore—laifukan da ke da hukunci ƙarƙashin Sashe na 97 na Kundin Dokar Laifi.

Haka nan, an zargi waɗanda ake tuhuma da yaki da gwamnati domin razana shugaban kasa, da kuma kai hari ga ‘yan sanda tare da ji musu rauni, ƙona ofisoshin ƴansanda, da kuma kai hari kan gine-gine daban-daban, ciki har da ginin Babbar Kotu, ginin Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), gidan buga jaridu na Kano, da kuma Gidan Gwamnatin Kano.

Comments
Loading...